Labarai
Asalin kwalejin share fagen shiga jamia ta CAS dake Kano mallakar kabilar Igbo ce
An bayyana asalin makarantar share fagen shiga jamia ta CAS a matsayin mallakar al’ummar Igbo a jahar Kano.
Daya daga cikin dattijan Najeriya kuma wanda yayi zamani da su marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto Alhaji Bello Ahmad Yakasai ne ya bayyana hakan a filin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyan Freedom da ya mayar da hankali a kan yadda Najeriya ta samu mulkin kai.
Bello Ahmad Yakasai yace dalilin yakin basasar Najeriya ne yasa Gwamnatin Jahar Kano karkashin marigayi Alhaji Audu Bako ce ta kwace makarantar ta CAS daga hannun kabilar Igbo ta koma hannun ta.
Bello Yakasai yace hadin kai da al’ummar Igbo suke da shi na nasu sai nasu ne yasa tun kafin Najeriya ta samu yanci a arewacin kasar suka mallaki makarantu domin ilmantar da ‘’ya ‘yan su.
Dattijo Bello Yakasai ya kara da cewa a lokacin da kungiyar Igbo union ta kafa makarantar ta CAs a shekarun 1954 matasa Hausawa basa samun damar zuwa karatu a makarantar ta CAS sai dai sukan halacci ajujuwa da yamma wanda ake wa lakabi da evening classes.
Yace daga cikin wadanda suka rika zuwa makarantar tare akwai marigayi tsohon Gwamnan jahar Kano Alhaji Aliyu Sabo Bakin Zuwo.
Da yake nasa tsokaci a shirin daraktan kula da cibiyar dab’I ta jamiar Bayero kuma mai koyar da kimiyyar siyasa a jamiar Farfesa Habu Muhammad Fagge yace daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta kafin da bayan samun yanci shi ne kabilanci da bangaranci wanda turawan mulkin mallaka sun taimaka wajen asassa shi.
Yace da al’ummar kasar nan zasu hada kai idan mutumin da ya kai shekara dari a wani yankin na Najeriya zai samu hakkin mallakar zama dan wannan yanki da kasar ta wuce haka a lamari na cigaba.