Labarai
Asusun ajiyar kuɗin waje na Najeriya ya ƙaru zuwa Dala Biliyan 52.66

Asusun ajiyar kuɗin waje na Najeriya ya ƙaru zuwa dala biliyan 52.66 ya zuwa ranar 19 ga Agusta, matakin da ya kasance mafi girma cikin sama da shekaru 17.
Bayanan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar ne suka nuna cewa ajiyar kuɗin ta ƙaru daga dala biliyan 45.56 da aka samu a ranar 2 ga Janairu zuwa dala biliyan 52.65 a ranar 19 ga Agusta.
Hakan na nufin ajiyar ta ƙaru da kusan dala biliyan 7.09, kwatankwacin kashi 15.6 cikin 100, cikin ƙasa da watanni takwas. Sabon adadin ya kuma zarce matakin dala biliyan 52.04 da aka samu a watan Yuli, yayin da CBN ya ce ajiyar ta ketare dala biliyan 52 a karon farko a wannan shekara a ranar 20 ga Yuli, lokacin da ta kai dala biliyan 52.02.
Adadin ya kasance mafi girma da aka samu tun Janairu 2009.
You must be logged in to post a comment Login