Labarai
Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙara wa’adin yin rijistar maniyyatan baɗi

Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano, ta ƙara wa’adin yin rijistar aikin Hajjin baɗi zuwa 31 ga watan nan da muke ciki na Agusta.
Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai.
Ya ce, ga duk maniyyacin da ke da niyyar yin aikin Hajjin na baɗi, zai iya fara ajeliye naira miliyan 6 kafin nan da ranar 31 ga watan Satumba mai kamawa ya cika sauran.
You must be logged in to post a comment Login