Connect with us

Labarai

Fetur din da ake shigo da shi Najeriya ya ƙaru a watan Yuli

Published

on

Man fetur da ake shigowa da shi kasar nan ya ƙaru a watan Yuli, yayin da samar da man daga matatun cikin gida ya ragu da kashi 21 cikin ɗari. Hakan ya sa ƙasar ta ƙara dogaro da man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.

 

Bayanan da suka fito daga kididdigar ayyukan bangaren man fetur na Najeriya na watan Yuli 2026, wadda aka wallafa a shafin hukumar da ke kula da harkokin man fetur a hukumance, sun nuna cewa samar da man cikin gida ya ragu daga lita miliyan 32.5 zuwa miliyan 25.8 a rana, yayin da shigo da man ya tashi daga miliyan 18.1 zuwa miliyan 19.7 a rana.

 

Jimillar man fetur da aka samu a ƙasar ya ragu da kashi 10, daga lita miliyan 50.6 zuwa miliyan 45.5 a rana. Haka kuma, yawan amfani da man ya ragu da kashi 25, daga lita miliyan 47.4 zuwa miliyan 35.7 a rana, yayin da adadin man da ake da shi a ajiye ya ƙaru daga abin da zai iya wadatar da ƙasar na kwanaki 19 zuwa 22.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!