Kiwon Lafiya
Asusun bada lamuni ya nuna damuwarsa kan ko Najeriya zata iya biyan bashin da ake binta
Asusun bayar da lamuni na Duniya IMF ya nuna damuwarsa kan ko Najeriya za ta iya biyan bashin da ake binta, sannan kuma ya bukaci gwamnatin tarayya ta fadada komar ta ta samar da kudaden shiga a cikin gida.
Asusun ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya ke gabatar da rahotonsa na al’amuran tattalin arzikin nahiyar Afirka na bana, wanda ya nuna yadda bashin ke kara taruwa.
Babban jami’in Asusun na IMF a kasar nan Amine Mati, ya ce kasashen da bashi ya yi wa katutu sun karu daga 6 a shekarar 2014 zuwa 8 a shekarar 2015, sannan suka sake karuwa zuwa 10 a shekarar 2016, yayin da yanzu su ka kasashe 15.
Har ila yau ya ce kudaden harajin kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida ya yi kasa matuka, inda ya bukaci a rubanya masu biyan harajin daga kashi 25 zuwa 50, wanda hakan zai kara bunkasa tattalin arzikin kasa da akalla kashi biyu cikin dari.
Bashin kasar nan dai ya kai Naira Tiriliyan 21 da biliyan 73 a karshen watan Disambar bara yayin da a cikin watan Yunin shekarar 2015 ya ke a mataki na Naira Tiriliyan 12 da biliyan 12.