Connect with us

Labarai

Asusun TETFund ya ware Biliyan 2 da rabi ga kowacce jami’ar Gwmamnati

Published

on

Asusun Tallafawa Manyan Makarantun kasar nan, TETFund, ya amince da ware kimanin Naira biliyan 2 da miliyan 530 ga kowace jami’ar gwamnati a ƙarƙashin shirin tallafawa manyan makarantu na shekarar 2026.

‎

‎Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin taron TETFund na yankin Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Lokoja.

‎

‎Ministan ya ce, baya ga jami’o’in gwamnati, TETFund ta ware Naira biliyan 1 da miliyan 870 ga kowace Kwalejin Kimiyya da Fasaha, wato Polytechnic.

‎

‎Haka kuma, an ware kimanin Naira biliyan 2 da miliyan 60 ga kowace Kwalejin Ilimi.

‎

‎Mohammed Idris ya ce kudaden na daga cikin shirin TETFund na tallafawa manyan makarantu domin inganta abubuwan more rayuwa, kayan koyarwa da sauran bukatun ilimi.

‎

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!