Connect with us

Labarai

Gwamnati ta yi watsi da ikirarin Atiku Abubakar na dawo da tallafin Mai

Published

on

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da alkawarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a 2027, tana mai cewa matakin zai iya mayar da Najeriya kan tsarin da ke jefa gwamnati cikin manyan basussuka da matsalolin kuɗi.

‎A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Alhamis, fadar ta ce Atiku ya sauya matsayinsa na baya kan tallafin mai ne saboda neman mulki.

‎Fadar ta ce Atiku ya taɓa goyon bayan cire tallafin, amma yanzu ya dawo da batun a matsayin wani babban alkawarin siyasa gabanin zaɓen 2027.

‎Sanarwar ta kuma yi tambaya kan yadda za a samu kuɗin biyan tallafin idan aka dawo da shi, musamman ganin cewa tsarin tallafin da ake amfani da shi kafin Mayun 2023 ya jefa gwamnati cikin manyan nauyin kuɗi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!