Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya naɗa sabon Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya

Published

on

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mista Abel Olumuyiwa Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

 

Sanarwar ta ce Enitan zai fara aiki ne daga ranar 27 ga Agusta, 2026, inda zai maye gurbin Didi Esther Walson-Jack, wadda za ta yi ritaya bayan ta kai shekarun ritaya.

 

Enitan,ya shafe shekaru bakwai da watanni bakwai yana rike da mukamin Sakataren Din-din-din a Ma’aikatar Harkokin ‘Yan Sanda, Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da kuma Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. A halin yanzu yana matsayin Sakataren Din-din-din a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

 

Shugaba Tinubu ya yaba wa tsohuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack, bisa irin gudunmawar da ta bayar wajen kawo sauye-sauye da sabbin dabaru a aikin gwamnati.

 

Ya kuma umurci Enitan da ya ci gaba da inganta sauye-sauyen da ake yi, tare da tabbatar da ƙwarewa, gaskiya, riƙon amana da ingantaccen aiki a cikin ma’aikatan gwamnati.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!