Labarai
ASUU-NWU ta buƙaci a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar shekerar 2025

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Northwest University da ke Kano (NWU), ta nuna damuwa kan jinkirin da ake samu wajen aiwatar da biyan wasu kuɗaɗen alawus-alawus da aka amince da su a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya a shekarar 2025.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yau Litinin 8 ga Yuni mai ɗauke da sa hannun shugabanta Kwamared Mansur Said da Sakatarenta Kwamared Yusuf Ahmed Gwarzo, ta bayyana cewa har yanzu ba a fara aiwatar da tsarin mai suna Consolidated Academic Tools Allowance (CATA) da kuma Secretariat Assistance Allowance (SAA) ba, duk da cewa an tsara fara aiwatar da su tun daga watan Janairun bana.
Ƙungiyar ta ASUU reshen jami’ar Northwest Kano, ta ce a yayin taronta na majalisar ƙoli da aka gudanar a ranar 3 ga Yunin bana, ta yi nazari kan halin da ake ciki dangane da wadannan alawus-alawus, inda ta nuna matuƙar damuwa kan rashin wani gagarumin ci gaba duk da rubuce-rubucen da ta gabatar wa mahukuntan jami’ar da kuma Gwamnatin jihar Kano.
Kungiyar ta jaddada cewa walwalar ma’aikatan jami’o’i na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, bunkasa aiki da ci gaban tsarin ilimi mai zurfi.
Ta kuma ce, jinkirin biyan hakkokin da aka amince da su na jefa ma’aikata cikin wahalhalu tare da haifar da taruwar bashin alawus-alawus da za a iya kauce wa idan aka dauki mataki a kan lokaci.
ASUU-NWU ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar matakan da suka dace domin fara aiwatar da tsarikan na CATA da SAA ba tare da bata lokaci ba.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa cika alkawurran da aka daukar wa ma’aikatan jami’o’i na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin gwamnati da ma’aikata, tare da bunkasa ingancin ilimi a manyan makarantu.
Haka kuma, kungiyar ta yaba da kokarin da wasu masu ruwa da tsaki ke yi wajen tattaunawa da gwamnati kan batutuwan da suka shafi walwalar ma’aikata, tare da bukatar su kara himma domin samun mafita cikin gaggawa.
Ta cikin sanarwar, Ƙungiyar ta ASUU reshen jami’ar ta Northwest Kano, ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da bin hanyoyin tattaunawa da fahimtar juna, tana mai fatan hukumomin da abin ya shafa za su dauki matakan da suka dace cikin gaggawa domin kare muradun ma’aikata, dalibai da daukacin al’ummar jami’ar.
You must be logged in to post a comment Login