Labarai
Shugaba Tinubu ya rantsar da Joseph Olasunkanmi a matsayin sabon Ministan Lantarki

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin sabon Ministan Wutar Lantarki, sannan ya rantsar da Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin Karamin Ministan Harkokin Waje. An gudanar da bikin rantsarwar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Litinin, tare da halartar iyalan ministocin da manyan jami’an gwamnati.
Nadin sabbin ministocin ya biyo bayan murabus din tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, domin ci gaba da harkokinsu na siyasa. Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabbin ministocin a ranar 6 ga Mayu, 2026.
Sabon Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, kwararre ne a fannin tattalin arziki da gyaran cibiyoyin gwamnati, yayin da Ambasada Sola Enikanolaiye tsohon jami’in diflomasiyya ne da ya yi aiki a ma’aikatar harkokin waje na tsawon shekaru 35, tare da wakiltar Najeriya a kasashe da dama.
You must be logged in to post a comment Login