Labarai
Kano: Ƴan sanda sun kama mutane 345 cikin Kwana 3

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce a sumamen data gudanar na kakkabe masu aikata muggan laifuka, a cikin kwanaki uku ta samu nasarar kama mutane dari uku da arbain da biyar.
Kwamishinan yan sandan jihar Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai.
Ya kuma ce, rundunar su ta Operation kukan kura na ci gaba da aiki kain da nain a jihar, kuma suna samun nasara.
You must be logged in to post a comment Login