Labarai
ASUU ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 4 don fara aiwatar sabon tsarin albashi

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta sake jaddada matsayinta kan sabon tsarin albashi da aka amince da shi, inda ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki huɗu domin fara aiwatar da shi nan take.
Shugaban kungiyar, Farfesa Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan a wajen wani taron lacca da aka gudanar a Jami’ar Sa’adu Zungur da ke jihar Bauchi.
Ya ce an cimma yarjejeniyar sabon tsarin albashin a watan Disamba na 2025, kuma an shirya fara aiwatarwa tun daga Janairu 2026,Sai dai ya ce har yanzu gwamnati ba ta cika wannan alkawari ba, abin da ya haifar da ci gaba da rikici da kuma barazanar yajin aiki a jami’o’i da dama a fadin ƙasar.
ASUU ta ce idan gwamnatin tarayya ta kasa fara biyan sabon tsarin albashin cikin wa’adin kwanaki huɗu da ta bayar, za ta ɗauki mataki mai tsauri.
You must be logged in to post a comment Login