Labarai
ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da gwamnoni da taɓarɓara fannin ilimi
Ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU, ta buƙaci gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaba Tinubu, da ta ɗabbaka yarjejeniyar ƙungiyar ƙwadago ta duniya da ƙasar nan ta kasance cikin waɗanda suka sanya wa hannu domin inganta fannin ilimi.
Shugaban shiyyar Kano na ƙungiyar Kwamared Abdulkadir Muhammad, ne ya buƙaci hakan yayin ganawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan da ƙungiyar ta kammala wani taron shugabanninta.
Kwamared Abdulkadir Muhammad ya ce, shiyyar Kano na ƙungiyar da ya haɗa da jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria da Jami’ar Bayero da jami’ar gwamnatin jihar Kaduna da jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.
Sauran du ne, Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse da jami’ar Yusuf mai Tama Sule da kuma jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, sun shirya taron ne domin ankarar da al’umma irin halin da suke ciki musamman kan irin yadda gwamnatin tarayya da jihohi suke janyo ko baya a fannin ilimi.
Haka kuma ya bayyana takaici bisa yadda gwamnatoci ba sa sakar wa jami’oi kuɗaɗen gudanarwa yadda ya kamata.
Shugaban ƙungiyar ta ASUU shiyyar Kano, ya kuma bayyana ragin kuɗin makaranta da gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi n kimanin kaso 50 da cewa babu abinda ya haifar illa ko baya.
Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya kuma ce, matukar gwamnatin tarayya da na jihohi ba su dauki matakin gyara kan wannan batu ba, to za su yi taron hukumar zartaswar ƙungiyar domin ɗaukar matakin da ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login