Labarai
Atiku da Obi sun ƙi goyon bayan ɗan takarar haɗakar ’yan adawa ɗaya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, sun yi watsi da kiran da ƙungiyar siyasa ta G-100 ta yi na ganin jam’iyyun adawa sun tsayar da ɗan takara guda ɗaya domin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Duk da cewa sansanonin Atiku da Obi sun amince da buƙatar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa, kowannensu na ci gaba da nuna aniyarsa ta neman takarar shugaban ƙasa.
Mai magana da yawun Atiku, Phrank Shaibu, ya ce Atiku ya wuce matakin tattaunawa kan taron haɗa kan ’yan adawa, yana mai cewa yanzu ’yan Najeriya ne za su yanke shawara bisa manufofin ’yan takarar.
A nasa bangaren, jam’iyyar NDC ta ce ba lallai ne ’yan adawa su tsayar da ɗan takara guda ɗaya ba domin kayar da APC. Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar, Osa Director, ya ce idan aka cimma matsayar haɗaka, jam’iyyar ta yi imanin cewa Peter Obi ne ya fi cancanta ya jagoranci ƙawancen.
Ƙungiyar G-100 dai na son a haɗa kan ’yan adawa domin kauce wa rarrabuwar ƙuri’u, inda ta shirya wani taron tattaunawa a ranar 31 ga Agusta.
You must be logged in to post a comment Login