Connect with us

Labarai

Atiku ya bukaci FBI ta fitar da bayanan Tinubu kan alaka da miyagun kwayoyi

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya bukaci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka, FBI, ta fitar da bayanan da take da su dangane da Shugaba Bola Tinubu, muddin doka ta ba da damar yin hakan.

Atiku ya ce ’yan Najeriya na da hakkin sanin tarihin da kuma halayen mutumin da ke neman sake rike mukamin shugaban kasar, musamman ganin yadda zaben 2027 ke kara karatowa.

Ta hannun mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, Atiku ya ce FBI za ta iya kare bayanan sirri da suka shafi binciken laifuka, ba tare da boye bayanan da za a iya bayyana wa jama’a bisa doka ba.

Ya kuma mayar da martani ga ikirarin cewa fitar da wasu bayanan na iya jefa rayukan mutane cikin hadari, inda ya ce ’yan Najeriya tuni suke fuskantar barazanar tsaro da matsin tattalin arziki.

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da aiwatar da manufofin tattalin arziki da suka kara tsadar sufuri, abinci, kiwon lafiya da sauran bukatun yau da kullum. Ya kuma ce matsalolin ta’addanci, ’yan bindiga, yunwa da tsadar rayuwa na kara jefa iyalai cikin wahala.

Ya jaddada cewa bukatar fitar da bayanan ba yunkuri ba ne na neman Amurka ta tsoma baki cikin siyasar Najeriya, sai dai neman tabbatar da gaskiya da rikon amana, yana mai cewa ’yan Najeriya na da damar binciken tarihin duk wanda ke rike da madafun iko.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!