Connect with us

Labarai

Manyan jam’iyyun adawa na shirin haɗa ƙarfi don tunkarar shugaba Tinubu a zaɓen 2027

Published

on

Manyan jam’iyyun adawar Najeriya na shirin haɗa ƙarfi domin tunkarar shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

 

Ƙungiyar G-100 ce ke jagorantar yunƙurin, inda take son haɗa ADC, PDP, NDC, PRP, SDP da APM, tare da samar da ɗan takarar da zai samu goyon bayan jam’iyyun.

 

Daga cikin ‘yan takarar akwai Atiku Abubakar da ga ADC sai Peter Obi, NDC kana Seyi Makinde a APM, da Donald Duke, daga SDP kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

 

Sai dai yunƙurin na iya fuskantar ƙalubale sakamakon bambancin ra’ayoyi da burin shugabannin jam’iyyun.

 

G-100 na shirin gudanar da taron tattaunawa a ranar 18 ga Agusta domin neman matsaya guda, bayan irin wannan yunƙuri ya gagara samar da haɗin kai a baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!