Connect with us

Labarai

Gobara ta hallaka Uwa da ‘Ya’yanta mata 3 a Yobe

Published

on

Wata mummunar Gobara ta tashi a Rugar Audu Badali da ke karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, inda ta hallaka wata mata da ‘ya’yanta uku. 

 

 Wadanda suka rasa rayukansu suka hada da Bilkisu, matar Mallam Bukar, da ‘ya’yanta Zainab, Hafsat da Salamatu.

 

Bayan faruwar lamarin, an yi jana’izar wadanda suka rasu bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da gobarar ta lalata gidan iyalan tare da dukiyoyinsu, lamarin da ya bar wadanda suka tsira daga cikin iyalan ba tare da matsuguni ba. 

 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe, SEMA, ta kai ziyara domin tantance irin barnar da gobarar ta yi da kuma gano bukatun gaggawa na iyalan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!