Labarai
Atiku ya bukaci a ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027 kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci a ayyana dokar ta-baci a kan harkokin tsaro saboda karuwar hare-hare kan makarantu da taɓarɓarewar tsaro a faɗin kasar nan.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Laraba bayan rahotannin harin da aka kai makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Iluke Bunu a karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi, inda aka ce mutane uku ciki har da mataimakin shugaban makarantar sun rasa rayukansu, yayin da aka yi garkuwa da wasu ɗalibai.
Ya nuna damuwar sa kan hare-haren makarantu inda ya ce ba wai kawai suna jawo asarar rayuka ba ne, har ma suna barazana ga ilimi da kuma makomar ci gaban kasar a nan gaba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi nuni da wasu hare-haren da suka gabata inda aka yi garkuwa da dalibai a wasu sassan jihohin Oyo da Borno, yana mai gargaɗin cewa ƙaruwar ire-iren waɗannan hare-haren kai tsaye kan cibiyoyin ilimi, babbar barazana ce.
A cewarsa, ci gaba da rashin tsaro a makarantu na iya hana koyarwa da koyo gudana yadda ya kamata, tare da haddasa tsoro da damuwa ga dalibai da malamai.
You must be logged in to post a comment Login