Connect with us

Labarai

Kogi: An shiga jimami a ƙananan hukumomin Kabba da Bunu bayan harin yan bindiga a makarantar sakandire

Published

on

An shiga jimami a ƙananan hukumomin Kabba da Bunu da ke jihar Kogi bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari makarantar sakandiren gwamnati ta Iluke Bunu, inda suka kashe mutane uku ciki har da mataimakin shugaban makaranta da wani yaro mai shekara shida.

 

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa makarantar ne da misalin ƙarfe goma na safe a kan babura kusan arba’in, da nufin yin garkuwa da ɗalibai da mazauna yankin. Sai dai jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da masu gadin sa-kai sun yi gaggawar isa wurin tare da fafatawa da maharan.

Rundunar ’yan sandan jihar Kogi ta ce an kashe ɗaya daga cikin maharan yayin musayar wuta, yayin da wani jami’in tsaro ya samu raunukan harbi. 

 

Haka kuma ta tabbatar da mutuwar Mataimakin Shugaban Makaranta, Malam Sunday Jacob Alhassan mai shekara 70 da kuma ƙaramin yaro Sunday Ayele mai shekara shida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!