Connect with us

Labarai

Mutuwar Janar Rabe abin kunya ne ga Najeriya – Atiku Abubakar

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce mutuwar tsohon Janar din soja, Major General Abubakar Rabe, a hannun masu garkuwa da mutane na nuna yadda matsalar tsaro ke kara muni a Nijeriya. Ya ce abin takaici ne jami’in da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare kasa ya mutu a hannun ‘yan ta’adda.

 

Atiku ya kuma danganta lamarin da sabon harin da aka kai a Chibok da kona makarantu, yana cewa hakan ya sake tayar da hankulan al’ummar da har yanzu ba su manta da sace daliban Chibok ba. A cewarsa, hare-haren na nuna cewa ‘yan ta’adda na ci gaba da barazana ga rayuka da kuma ilimi.

 

Dan takarar shugaban kasa na ADC ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa kan matsalar tsaro, yana mai cewa lokaci ya yi da za a wuce alkawura zuwa daukar matakai masu tasiri domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!