Labarai
Canada ta sanya dokar hana ‘yan kasa da shekaru 16 mallakar shafukan sada zumunta.
Canada ta sanya dokar hana ‘yan kasa da shekaru 16 mallakar shafukan sada zumunta.
Gwamnatin ta kuma bukaci kamfanonin da ke bayar da izinin bude shafukan sada zumunta da su tabbatar da cewa sun bi dokar sau da kafa. Kazalika dokar ta kuma shafi amfani da fasahar kirkira ta AI.
Ministan raya al’adu na kasar Marc Miller, ya ce tabbas sun gaza wajen sauke nauyin kula da matasa masu tasowa, kuma dole ne a yi wa tufkar hanci don bai wa yaran kariya daga duk wata barazana.
Sabuwar dokar ta kunshi sassa akalla guda bakwai da suka hada da bai wa yara kariya ta hanyar kare mutuncinsu da cin zarafi da tsattsauran ra’ayi da ta’addanci da dai sauransu.
Canada dai ta kasance ta hudu da ta haramtawa matasa masu tasowa ‘yan kasa da shekara 16 amfani da shafukan sada zumunta, baya ga Australiya da Brazil da Indonesiya
You must be logged in to post a comment Login