Labarai
Atiku ya halarci kotu a shari’ar da ya ke kalubalantar nasarar Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyara PDP a zaɓen bana Alhaji Atiku Abubakar, ya halarci zaman kotun da ake ci gaba da gudanrwa a yau Alhamis kan kalubalantar nasarar da sabon zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu.
Tun a ranar Talata ne kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage zaman da ta fara domin ci gaba da zaman share fage a kan ƙorafe-ƙorafe game ta nasarar Bola Ahmed Tinubu.
Alƙalan kotun, sun tsara sauraron ƙorafe-ƙorafe daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar, a yau Alhamis da kuma korafin jam’iyyar LP.
Kotun ta fara zaman sauraron ƙararraki a kan nasarar Bola Ahmed Tinubu ne mako uku dai-dai kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasan.
Masu ƙorafi huɗu ciki har da manyan ‘yan adawan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, kowannensu ke iƙirarin shi ne ya kamata INEC ta ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun bana.
You must be logged in to post a comment Login