Labarai
Atiku ya rungumi kaddara
Dan takarar shugaban kasa a babban zaben kasar nan da aka yi a ranar 23 ga watan Fabarerun da ya gabata a jam’iyyar Adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya hakura bayan da kotun koli ta ta yanke hukuncin yin watsi da karar da shigar gaban ta.
Atiku Abubakar yace ya hakuri ganin damar da yake da ita tazo karshe na neman hakkin sa a kotun Kolin kasar nan.
Atiku Abubakar ya wallafa hakan ne a shafun sa nan Twitter cewa “yayi imanin ncewar Allah ne Abun dogoro kuma ‘yan Najeriya sun dogara ne akan zaben sun a Dumukuradiyya, dole ne na amince cewa zaben da na dauka akan shari’a ya zo karshe’’
A jiya ne dai Kotun Kolin kasar ta fara sauraron daukaka karar da Atiku Abubakar ya shigar a gabanta, yayin da yake kalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a babban zaben da aka yi a wannan shekara ta 2019.
Kotun Koli tayi watsi da karar Atiku
Atiku ya musanta ikrarin jami’yyar APC cewa bai cancanci tsayawa takara ba
Atiku:ya nemi kotu ta ayyana shi ya lashe zabe
Sai dai Kotun koli ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takarar ta, Atiku Abubakar suka shigar suna kalubalantar nasarar da aka bayyana abokin takararsa, Muhammadu Buhari ya yi a zaben da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara.
Alkalin Alkalan babbar kotun Najeriya, mai shari’a Tanko Muhammad da ya jagoranci alkalan babbar kotun su shida ya sanar da hukunci kan shari’ar cikin sadarori uku da suka kawo karshen duk wata takaddama kan wancan zabe.
Babban Alkalin Alkalan na kasa ya bayyana cewa sai a nan gaba za a bayyana dalilan da ya sanya alkalan suka yanke wannan hukunci.
Ya kara da cewa makonni biyu suka yi shi da sauran alkalan suna karanta dukkan bayanai da kuma shaidun da aka gabatar kan karar, inda suka lura da rashin madogara a karar.
An yanke wannan hukunci da dukkan Alkalan su shida suka amince da shi cikin abin da bai kai Awa guda ba, bayan da kotun ta saurari bayanan daukaka kara daga bakin mai gabatar da kara.