Addini
Ba a samu rahoton ganin watan Muharram ba – Sarkin Musulmi
Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Talata a matsayin 1 ga watan Muharram na sabuwar shekara.
Wannan ya biyo bayan rashin samun rahoton ganin wata a ranar Lahadi 29 ga watan Zul-hajj.
Sarkin musulmi ya ce, kwamitin duban wata bai samu labarin ganin wata daga kowanne bangare ba, a don haka watan Zul-hajj zai cika kwanaki 30.
Alhaji Sa’ad Abubakar yana mai cewa, sabuwar shekarar musulunci ta 1443 za ta fara daga ranar Talata 10 ga watan Agusta, a matsayin 1 ga watan Muharram 1443.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini Farfesa Sambo Wali ya fitar, tare da bukatar al’ummar musulmi su ci gaba da yiwa kasa addu’o’in zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login