Labarai
Ba Buhari ne kaɗai da haƙƙin tsaron ƙasar nan ba – Nanono
Ministan Noma na ƙasa Alhaji Sabo Muhammad Nanono ya ƙalubalanci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi kan matsalar tsaro a Najeriya.
A wata zantawa da ministan yayi da sashen Hausa na Radio France International kan yadda matsalar tsaro ta shafi ɓangaren noma.
Ministan ya ce “magana ta Allah da Annabi ba gwamnatin tarayya ce ta ke da haƙƙin tsaron wannan abu kawai ba, gwamnatocin jihohi ƙananan hukumomi, in ka tafi ƙasa har Dagatai da masu unguwanni, ya aka yi suka sake suka bar wannan yanayi na tsaro ya zama abin da ya zama, amma kowa ya tashi sai ya ce gwamnatin tarayya”.
“Eh gwamnatin tarayya tana da haƙƙin ta tsare rayuwa na jama’a, amma ai su waɗannan da suke kusa da waɗannan mutanen su ya kamata tun da farko ma su fara maganar cewa muna ganin muna da matsala a kan waɗannan abubuwan”.
Alhaji Sabo Nanono ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya tana iya ka ƙoƙarinta wajen bunƙasa noma da samar da abinci a ƙasar nan.
Labarai masu alaƙa:
Sabo Nanono ya maida martini kan zargin da ake masa
You must be logged in to post a comment Login