Connect with us

Labaran Wasanni

Dan wasan Najeriya ya kamu da Corona

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Paul Onuachu dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Genk dake kasar Belgium ya kamu da cutar Corona a gwajin da a ka gudanar ga ‘yan wasan dake buga wasa a kasar.

Sai dai sakamakon da a ka samu na ‘yan wasan kasar nan da suma suke wasa a kungiyar Heracles Almelo dake kasar ta Belgium wato Stephen Odey da Cyril Dessers ya nuna cewar basa dauke da cutar.

Paul Onuachu mai shekaru 26 shi ne dan wasan farko na kungiyar kwallonn kafa ta kasa Super Eagles da a ka samu dauke da cutar ta Corona cikin ‘yan wasan kungiyar dake wasa a kasashen ketare da a ka yi mu su gwajin cutar a kungiyoyin su.

Onuachu yabar kasar nan zuwa kasar ta Belgium a ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata, domin halartar kungiyar sa a kasar ta Belgium.

Onuachu dai shi ne dan wasa na biyu a kasar nan da ya kamu da cutar, tun bayan da Akpan Udoh, ya kamu da cutar a watan Fabrairun da ya gabata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,887 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!