Kasuwanci
Ba gudu ba ja da baya kan binciken zargin badakalar sayar da filin masarautar Kano na Dorayi – Muhyi Magaji
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta ce, ba za ta dakatar da binciken da ta ke yi ba game da batun sayar da da filin gidan Sarki na Dorayi da ke yankin karamar hukumar Gwale.
A cewar Muhyi Magaji Rimingado hukumar za ta ci gaba da binciken zargin badakalar, har sai gaskiya ta yi halinta.
Muhyi Magaji Rimin Gado ya yi wannan jawabi ne a ranar juma’a, yayin ganawa da manema labarai, yana mai cewa hukumar ta samu korafin sayar da katafaren filin ne daga kungiyar ci gaban unguwar Dorayi babba.
Ya ce, tun da fari masu ruwa da tsaki kan filin ne suka bukaci gwamnati ta basu damar gina wurin shakatawa da kuma wurin zuba shara, sai dai daga bisani aka gano cewa cefanar da filin su ka yi, tare da karkatar da kudin zuwa biyan buktaun wasu daidaikun mutane maimakon sanya kudin cikin asusun masarautar Kano.
‘‘Duk da cewa mutanen da su ka sayi filin sun kai ni kara kotu, amma hakan ba zai hana hukumar ta anti-corruption ci gaba da gudanar da bincike ba, don bankado almundahanar da take zargin an aikata wajen sayar da filin’’
‘‘Ko a yau Juma’a mun gano cewa an ci gaba da gudanar da gine-gine a cikin filin wanda hakan ta sanya muka garzaya wajen muka gabatar musu da takardar kotu da ta haramta ci gaba da aiki a fili’’ a cewar Muhyi Magaji Rimingado.
You must be logged in to post a comment Login