Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashawa: Mataimakin gwamnan Kano ya faɗa komar zargi

Published

on

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta ce ta karɓo kuɗi har miliyan bakwai da aka karkatar da su a ma’aikatar noma ta jihar Kano.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Muhyi ya ce, ma’aikatar Noman na karɓar kuɗaɗen haraji a hannun manoma domin ba su damar yin noma a filayen noma na gwamnatin Kano, sai dai kuma ana karkatar da kuɗaɗen.

Ya ƙara da cewa, baya ga miliyan bakwai da suka karɓo, yanzu haka su na tsaka da bincike kan wasu kuɗaɗen har sama da miliyan bakwai da aka yi zargin su ma an karkatar da su a ma’aikatar.

Yace, wannan ya saɓa da sashe na 26 na dokar hukumar a don haka ya zama dole su ɗauki mataki a kai.

Muhyi ya ce, yanzu haka suna ci gaba da bincike kuma har sun gayyaci manyan ma’aikata a ma’aikatar noman tun daga kan babban sakatare har zuwa daraktoci.

A ƙarshe ya ce, binciken su zuwa yanzu bai nuna cewa akwai hannun kwamishinan noma na Kano ba, wanda shi ne mataimakin gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Muhyi ya ƙara da cewa, mataimakin gwamnan yana bada haɗin kai wajen binciken da ake gudanarwa game da wannan badaƙala.

Ku kasance da shirin An Tashi Lafiya da ƙarfe 6 na safiyar yau Talata domin jin cikakken labarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!