ilimi
Ba jihar Bauchi ba ce ke da yawan yaran da basa zuwa makaranta ba -Ma’aikatar ilimi
Ma’aikatar ilimin Najeriya ta ce labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa jihar Bauchi ita ce ke kan gaba da adadin yaran da basa zuwa makaranta, ba gaskiya bane.
Sakataren yada labaran ma’aikatar Ben Goong, ne ya bayyana haka, yayin da yake zantawa da manema labarai jiya Juma’a a Abuja.
Marasa kishin kasa da son lalata harkar ilimi ne suka fitar da wata kalandar bogi – Ganduje
Goong, ya ce wadanda ke wallafawa labarin cewa yara miliyan 1 da dubu 239 da dari 759 ne ke gararamba akan titunan jihar Bauchi, suna yin hakan ne don zubar da kimar ma’aikatar ilimi.
Haka kuma ya bukaci daukacin al’umma da su yi watsi da irin wadandan labarai na karya a cewar sa ba su da fa’ida.
You must be logged in to post a comment Login