Labarai
Ba ma bukatar sanya Solar -‘yan kasuwar Sabon gari
A baya-bayan nan ne dai jagorancin kasuwar Sabon gari, ya samar da tsarin wutar lantarki da hasken rana na Solar a fadin kasuwar dan gujewa afkuwar gobara.
Sai dai a safiyar litinin din nan wasu daga cikin al’ummar dake gudanar da kasuwanci a cikin kasuwar ta daga bangarori da dama suka gudanar da zanga-zanga dangane da samar musu da wutar solar a cikin kasuwar.
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar ta Abubakar Rimi Kenan da akafi sani da kasuwar sabon gari lokacin da suke gudanar da zanga-zanga game da samar da wutar solar da shugabancin kasuwar zaiyi.
Haka kuma mazauna kasuwar ta Sabon gari sun nuna rashin amincewar su game da karbar naira dubu goma duk shekara a hannun ‘yan tebura da kuma tsarin bude kasuwa da karfe tara na safiya, inda suka nuna rashin amincewar su kan al’amarin.
Wasu daga cikin mutanan da suka gudanar da zanga-zangar cikin kasuwar sun bayyana rashin jindadin su inda suka yi kira ga gwamnatin jihar Kano data sanya baki kan lamarin.
Kan koken nasu ne ya sanya muka tuntubi shugaban kasuwar ta Abubakar Rimi wato Sabon gari Alhaji Ubah Zubairu game da lamarin, inda yace sun samar da wutar solar ne sabo da magance-afkuwar gobara a kasuwar.
Yace daukan matakin bude kasuwar da karfe tara na safiya ya biyo bayan korafe-korafe da wasu daga cikin ‘yan kasuwar keyi ana yi musu sake-sake idan aka bude kasuwar da wuri.
Alhaji Ubah Zubairu ya kara da cewa adon haka duk wata doka da kasuwar ta samar ta samar da itane dank are rayuka da dukiyoyin al’ummar dake cikin kasuwar, adon haka dokoin da suka sanya a kasuwar sunanan yadda suke bazasu sauya ba.
You must be logged in to post a comment Login