Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ba mu gamsu da fitowar baki yin rijista a jihar Kano ba- Hukumar kula da shige da fice

Published

on

Kwanturollan hukumar kula da shige da fice ta kasa dake nan Kano Dikko Nuhu Yashe yace babban kalubalen da hukumar ke fuskanta a yanzu shi ne rashin fitowar  yan kasashen waje mazauna Kano domin yin rijista.

Dikko Nuhu Yashe ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Kano a yayin bikin cin abincin dare da hukumar hana shige da fice ta kasa dake nan Kano ta shirya na karshen shekara domin karrama jami’anta .

Ministan cikin gida ya gana da shugabannin jami’an tsaro don magance rikicin makiyaya a jihar Filato

Dikko Nuhu Yashe yace tun da aka fara rijistar shedar bakin ‘’yan kasashen waje ake samun matsaloli na kin fitowar baki mazauna Najeriya musamman ma na nan jihar Kano.

Hukumar shige da fice ta ja kunnen wasu jamianta kan cin hanci

Dikko Nuhu Yashe yayi kira gare su da su tashi tsaye wajen ganin an yi musu rijista saboda muhimmancin ta .

Dikko Nuhu Yashe ya kara da cewa a cikin wannan wat ana Janairu wa’adin yin rijistar zai kare idan suka fito suka yi zai amfane su da su da al’ummar kasa.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!