Connect with us

Labaran Kano

Marigayi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero yana Kallan wasan kwaikwayon Hankaka

Published

on

An bayyana marigayi mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a matsayin daya daga cikin mashahuran mutanan dake kallan wasan kwaikwayo na hankaka.

Babban jarumin shirin Muhammad B Umar wanda aka fi sani da Hankaka ne ya bayyana haka a wata tsohuwar tattaunawa da muka yi da shi.

Hankaka ya shaida min cewa wani lokacin ko Marigayi Alhaji Ado Bayero bai samu kallan shirin ba ana aikowa domin a karbar masa kwafi.

Muhammad bin Umar Hankaka ya kara da cewa shima shararran malamin Addinin musuluncin nan kuma Marigayi Wazirin Kano Sheikh Isa Waziri yana daya daga cikin masu kallan shirin wasan kwaikwayon na Hankaka.

Shirin wasan kwaikwayo na Hankaka ana gabatar da shi ne a gidan Talabijin na ARTV wanda tun lokacin yana gidan talabijin na CTV 67.

Shirin wasan kwaikwayo na Hankaka ya yi shuhura sakamakon barkwanci dake cike da shirin da kuma nishadantarwa.

Shirin wasan kwaikwayon na Hankaka yayi tashe a shekarun 1990 har zuwa shekarun 2000.

 

 

Labaran Kano

Shin me zaku iya tunawa game da rayuwar marigayi jarman Kano

Published

on

A yau ne shahararran dan kasuwar nan da ya samar da kamfanin Jirgin sama mai zaman kansa na farko a kasar nan marigayi Alhaji Muhammad Adamu Dan Kabo ke cika shekaru goma sha takwas da rasuwa.

Marigayi Dan Kabo dai ya kasance mutum jajirtacce mai son ci gaban al’umma da kuma tallafawa tattalin arziki, wanda rashin say a zama babbar asara ga al’umma baki daya.

An dai haifi marigayi Alhaji Muhammad Adamu Dan Kabo a ranar uku ga watan Afrilun shekarar 1942, a karamar hukumar Kabo dake nan jihar Kano, inda yayi karatun Alkur’ani a garin na Kabo.

Alhaji Dan Kabo ya kasance dan kasuwa da ya samar da masana’antu daban- daban a kasar nan tare da samar da jirgin Sama na Kabo Air a shekarar 1980 wanda ya fara aiki a shekarar 1981.

Kafin rasuwar tasa kamfanin jirgin sama na Kabo ya mallaki jirage guda Ashirin da suke aiki da jigilar mutane a kwacce rana a sassan kasar nan musamman ‘yan kasuwa dake gudanar da kasuwanci a nan jihar Kano tare da tafiye tafiye dan shigo da kaya wanda hakan yasa kasuwancin jihar Kano ya habbaka tare da yin dai-dai da kasuwancin zamani.

Da ya ke jawabi Laftanan Kanal mai ritaya Daudu Sulaiman da ya kasan ce aboki ga marigayi Dan Kabo lokacin da yana raye ya ce, marigayi Muhammadu Adamu Dan Kabo mutum ne mai matukar son jama’a da son ci gaban su, wanda kuma ya kasance mutum mai alkahiri ga jama’a,wanda dukiyar sa bata rufe masa idanu ba.

Da yake jawabi game da yadda marigayi Dan Kabo ya gudanar da rayuwar sa tsohon shugaban tsangayar koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero Farfesa Balarabe Maikaba da ya rubuta littafi kan rayuwar marigayin cewa yayi kamata yayi gwamnati ta farfado da kamfanin na Dan Kabo duba da yadda ya durkushe a halin yanzu, don samar da kudin shiga ga jihar Kano, tare da sanya sunan sa a wasu gurare da za’a dinga tunawa da shi, la’akari da ayyukan alkhairi da ya gudanar a lokacin yana raye.

Hasiya Muhammad Adamu Dan Kabo itace kasance babbar ‘ya ga marigayin ta ce mahaifin ta mutum ne da baya nuna banbanci a tsakanin yayan sa da ‘ya’yan wasu daban, kuma ya sadaukar da rayuwar sa wajen tallafawa duk mutumin daya fuskanci yana cikin matsi na rayuwa a ko’ina yake.

Al’ummar jihar Kano da dai na ci gaba da bayyana cewa lokacin da Dan Kabo na raye ya bada gudun mawa sosai ga musulman kasar nan wajen saukaka musu kudin jirgi lokaci tafiya aikin hajji da umrah wanda hakan babban  abin a yaba ne da kuma samun tarin lada.

A ranar hudu ga watan Afrilun shekarar 2002 ne dai aka wayi gari da samun labarin rasuwar Dan Kabo, kwana daya Tsakani da lokacin bayan da aka gudanar da bikin cikar sa shekaru 60 da haihuwa, wanda mutuwar tasa tazowa al’ummar kasar na a bazata, ta kuma tilasta musu shiga cikin halin dimuwa.

 

Continue Reading

Labaran Kano

Wata mata ta zargi makociyarta da maita a Kano

Published

on

Wata mata mai suna Rabi Muhammad mazauniyar unguwar Farawa dake nan Kano, ta zargi wata makociyar da kama kurwar ‘yar ta mai suna Shema’u.

Rabi Muhammad ta yi zargin cewa makociyar ta mai suna Tine Usman tana zuwar wa ‘yar ta Shema’u dauke da wuka a mafarki, sannan tana ikrarin kashe ta.

Akan hakan ne ya sanya wasu matasa masu fushi da fushin wani su kayi yunkurin farwa Tine Usman da ake zargi, sai dai ‘yan sanda sun kai mata dauki inda suka dakatar da yunkurin matasan.

Sakamakon hakan ne ‘yan sanda suka tura yarinyar asibiti domin ayi mata gwaje-gwaje wanda a karshe aka gano cewa babu wata maita hassalima zazzafan zazzabin Trypot da Malaria ne ke damun ta.

A karshe dai ‘yan sandan Farawa sun aika da wannan dambarwa zuwa gaban kotu, inda za a fara sauraron karar nan bada jimawa ba.

Continue Reading

Labaran Kano

An cafke wani matashi saboda labaran karya kan Coronavirus a Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Mustapha Hamisu Aliyu shugaban kungiyar masu gidajen abinci ta Kano.

An cafke Mustapha ne sakamakon kirkira da yada labarin cewa wai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano ya bashi umarnin ya sanar da rufe dukkanin gidajen abinci dake Kano.

Shima a nasa bagaren Mustapha Hamisu ya ce wannan abu da ya fada tuntuben harshe ne yayi, kuma yana neman afuwar rundunar ‘yan sanda da ta yi masa afuwa sakamakon wannan abu da ya aikata.

Tun a jiya ne dai, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bakin kakakinta DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ta ce wannan labari karya ne wanda ba shi da tushe balantana makama, a don haka ta roki jama’a suyi watsi da shi.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,348 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!