Labarai
Ba sani ba sabo ga duk wanda ya taka dokar tsaftar muhalli – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata samar da hukunci mai tsauri ga direbobin adaidaita sahu dama ɗaiɗaikun jama’a wadanda su ke karya dokar fita a ranakun tsaftar muhalli na karshen kowane wata.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala zagayen duban tsaftar muhalli a titunan jihar Kano.
Ya ce, kowane wata sun lura da yadda direbobin babura masu ƙafa uku ke watsi da dokar hana zirga-zirga a lokacin tsaftar muhallin, duk da yarjejeniyar da ake ƙullawa tsakanin ma’aikatar muhalli da shugabannin su.
Getso, ya ƙara da cewa, har yanzu mutane ba su ɗauki tsaftar muhalli da muhimmanci ba ta yadda su ke yawace-yawace a gari a lokacin da ya kamata su tsaftace muhallansu.
Wasu direbobin babura masu ƙafa uku da suka karya dokar a yau sun gurfana a gaban kotun tafi da gidanka karkashin mai sharia Auwal Yusuf Sulaiman.
Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa, ma’aikatar muhalli ta yabawa al’ummar unguwar Ƙofar Nai’sa bisa gudanar da aikin gayya da su ka yi a safiyar yau.
You must be logged in to post a comment Login