Labaran Wasanni
Ba tabbas akan injin motocin tsere na Ferrari
Mahukuntan gudanar da gasar tseren motoci na Formula 1, sun ce basu da tabbas akan cewar injin motocin kamfanin Ferrari sun cika sharuda , kasancewar bin diddigin hakan abu ne mai wahala matuka.
Hakan ya biyo bayan zargin da wasu kungiyoyin gasar guda bakwai suka shigar gaban hukumar tsara gasar FIA, inda suka nuna rashin jin dadin su da halin ko in kula da akayi da lamarin.
Labarai masu alaka.
Dalilan dakatar da wasanni a birnin Tokyo
Aruna Quadri ya tafi jinyar rauni na mako uku
Sai dai hukumar ta FIA, ta bayyana matsayar ta in da tace duk wani mataki da za’a dauka da kuma bincike ba zai iya karkarewa a kusa ba, kasancewar ba cikakku kuma gamsassun hujjoji na karya ka’idojin yin gasar da kamfanin na Ferrari ya yi.
A larabar data gabata, kungiyoyin bakwai a sanarwar da suka fitar sun nuna rashin jin dadin su dangane kamfanin Ferrari, in da suka kara dacewa rashin bincika lamarin zai saka musu shakku kan , jagoranci nagari, adalci da tsari na hukumar ta keyi.
Haka kuma, sun kara da cewa suna da ikon a yi musu bayani dalla-dalla dangen da zargin su wada hakan kadai zai cire shakkun dake tattare dasu.
You must be logged in to post a comment Login