Labarai
Ba za a iya more Dimokuraɗiyya ba sai da tabbataccen tsaro – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi ƴan najeriya da su ƙaunaci Najeriya duk da irin matsalolin da ƙasar ke fama da su musamman matsalar tsaro.
A jawabinsa na ranar dimokraɗiyya, Tinubu ya ce a daidai lokacin da ƙasar ke murnar cikarta shekaru 27 da mulkin dimokraɗiyya ba tare da samun tangarɗa ba, abubuwa biyu marasa daɗi sun faru da suka haɗa satar yara ƴan makaranta a Oyo da Borno.
Tinubu ya ce dimokraɗiyya ba tare da tsaro ba to tamkar ba ta yi ƙwari ba, inda ya ƙara da cewa hakan ne “ya sa gwamnatin ta ayyana ta-ɓaci kan matsalar tsaron sannan kuma ta amince ɗaukar ƴan sanda fiye da 50,000 da kuma dubban sojoji.
Daga ƙarshe Tinubu ya jinjina wa marigayi Alhaji Mashood Abiola wanda ake bikin ranar saboda shi wanda ya ce ya yi siyasa kuma ya samu goyon bayan jama’a daga ɓangarorin addini da na al’adu daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login