Labarai
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da manoma a kasuwar Sabon Birni da ke Sokoto

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama bayan sun tare hanyar da ta nufi kasuwar Sabon Birni a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Shaidu sun ce maharan sun kai harin ne da safiyar ranar Laraba, inda suka iso kan kusan babura 20 tare da buɗe wuta kan matafiya, manoma da ‘yan kasuwa da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako. Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum 20 aka sace yayin harin, yayin da aka tafi da wasu cikin daji a kan babura, wasu kuma a ƙafa bayan an ɗaure su bibbiyu.
Daily Trust ta ruwaito cewa daya daga cikin mazauna yankin ya ce maharan sun kai harin ne a yankin Mangwaron Bullun, wata mahadar hanyoyi da ke haɗa al’ummomi da dama, ba tare da shiga cikin garin Sabon Birni ba. Haka kuma, wani matashi mai suna Abdurrashid ya bayyana cewa mahaifiyarsa na cikin waɗanda aka sace yayin da take aiki a gona.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro da wakilin Sabon Birni a majalisar dokokin jihar Sokoto ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba. Harin na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kashe-kashe ke ci gaba da addabar sassan jihar Sokoto.
You must be logged in to post a comment Login