Labaran Freedom
Ba za mu bari ayi amfani da miyagun kwayoyi yayin babban zabe ba-NDLEA
- Ba zamu bari ayi amfani da miyagun kwayoyi a babban zaben kasa da ke tafe ba
- Duk wanda muka kama da shigo da kwayoyi za’a kama shi
- Duk wanda ta kama kuma yana shaye-shaye shima za’a kamashi
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen Jihar Kano, ta ce, ba za ta bari ayi amfani da miyagun kwayoyi a babban zaben kasa da ke tafe ba’.
Shugaban hukumar Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radiyo.
Ya ce, za su yi amfani da hanyoyin ba sani ba sabo akan duk wanda aka kama da shigo da kwayoyi, ko raba su a waje kafin zabe da lokacin zabe za ta kama shi.
Kwamandan Abubakar Idris ya kara da cewa hukumar bazata saurarawa duk wanda ta kama yana shaye-shaye ba, ta hanyar kama su, tare da hukunta su dai-dai da laifinsu.
RAHOTO: Hafsat Abdullahi Danladi
You must be logged in to post a comment Login