Kimiyya
Ba za mu yafewa Najeriya bashi ba – IMF
Mambobin hukumar gudanarwar asusun bada lamuni na duniya (IMF) sun ki amincewa su sanya sunan Najeriya cikin kasashe 28 wadanda asusun na IMF zai yafe musu kudin ruwa na bashin da ya ke binsu.
Hukumar gudnarwar sun amince a yafe bashi ga wasu kasashe 28 wanda shine irinsa karo na uku tun bayan bullar cutar corona.
Da farko dai asusun na IMF ya fara daukar matakin ne a ranar 13 ga watan Afrilun 2020 kafin ya sake daukar matakin na biyu a ranar 2 ga watan Oktoba 2020.
Kasashe da zasu amfana da tagomashin na asusun IMF sun hada da: Afghanistan, Jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Burundi, Jamhuriyar Afurka ta tsakiya, Chadi, Comoros, Jmahuriyar Dimukuradiyar Congo, Congo, Dibouti, Ethiopia, da kuma Gambia.
Sauran sune: Guinea, Guniea-BISSAU, Haiti, Liberia, Madagascar, Malawi, Mali, Mozambique, Nepal, Jamhuriyar Nijar, Rwanda, Sao Tome and Princpe, Saliyo, Solomon Island, Tajikistan, Togo da kuma Yemen.
A cewar shugabar asusun na IMF Kristalina Georgieva ta ce kasashen da aka yafewa sune su ka fi dandana kudarsu sakamakon cutar corona.
You must be logged in to post a comment Login