Kiwon Lafiya
Babbar kotun jihar Katsina ta tsayar da 10 da 11 ga watan Afrirun don sauraron karar da EFCC ta shiga kan tsohon gwamnan jihar
Babbar kotun jihar Katsina ta tsayar da ranar 10,11 da kuma sha biyu ga watan Afrilun shekarar da muke ciki don ci gaba da sauraron karar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta shigar gabanta tana karar tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shema.
Hakan na zuwa ne bayan da wata kotun daukaka kara dake zaman ta a Kaduna ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan ya shigar gabanta ya na bukatar kotun ta dakatar da tuhumar da ake yi masa a babbar kotun da ke zamanta a Jihar ta Katsina.
Ana dai zargin tsohon gwamnan jihar ta Katsina da wasu mutane guda uku da suka hadar da Sani Hamisu Makana, da Lawal Ahmad Safana, da kuma Ibrahim Lawal Dankaba da badakalar wasu kudade da yawan su ya kai naira biliyan 11 inda kuma aka gurfanar da su gaban mai shari’a Mai-Kaita Bako na babbar kotun jihar Katsina.
Tun a ranar 26 ga watan Satumbar shekarar 2016 ne hukumar EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo inda kuma a wancan lokacin ta bayyana cewa ana zargin sa da badakalar kudade da ya wansu ya kai naira biliyan 76, yayin da ta kara da cewa ta ayyana neman nashi ruwa a jallo ne sakamakon gayyatar sa da ta sha yi amma ya ki amsa gayyatar.