Kiwon Lafiya
Babbar kotun tarayya a Abuja tayi watsi da bukatar wata kungiya kan shugaba Buhari
Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar da wata kungiya ta yi na bayyanawa ‘yan-kasa adadin kudaden da aka kashewa shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake jinya a kasar waje.
Alkalin Kotun mai Shari’a John Tsoho ya yanke hukuncin cewa sashe na 14 (1) (b) na dokar ‘yan-cin samun bayanai ta Freedom of Information Act ya yi tanadin cewa shugaban kasa ne kadai zai iya sahale bada wadannan bayanai na kudin da aka kashe.
Wata kungiya mai rajin kare hakki da kuma ci gaban al’umma ta the Advocacy for Societal Rights Advancement and Develovement Initiative ta bukaci babban Bankin kasa CBN ya bada bayanan kudaden da aka kashewa shugaban kasa lokacin da ya ke jinya a ketare.
Har ila yau kungiyar ta nemi a cikakken ba’asin kudaden da aka kashe na kula da Jirgin shugabn kasa da kuma ‘yan tawagarsa.
A martanin da babban Bankin na CBN ya yi, ya aikewa fdar shugaban kasa ta hannun Ofishin shugaban ma’aikatan fadar Abba Kyari bukatar kungiyar, wanda hakan ya fusata kungiyar har ta garzaya Kotun don ganin ta tilastawa gwamnan CBN din fitar da bayanan.