Labarai
Babbar kotun tarayya ta yi watsi da ƙarar PDP ɓangaren Turaki

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu shugabannin jam’iyyar PDP suka shigar domin tilasta wa hukumar zaɓe ta INEC, ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.
Alƙali Salim Ibrahim ya yanke hukuncin cewa masu shigar da ƙarar ba su da hurumin gabatar da ƙarar. Saboda haka kotun ta ce ba ta da ikon sauraron shari’ar.
Alƙalin ya ce masu ƙarar sun kasa tabbatar wa kotu cewa INEC ta taɓa amincewa da kwamitin riƙon ƙwaryar da suke goyon baya, ko kuma cewa suna da ikon shigar da ƙara a madadin jam’iyyar PDP.
Shugaban kwamitin amintattu na PDP tsagin Turaki ƙarƙashin Sanata Adolphus Wabara, tare da wasu mambobin kwamitin ne suka garzaya kotu suna neman a umarci INEC ta sabunta bayananta tare da amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.
Sun kuma buƙaci kotun ta umarci hukumar zaɓen ta wallafa sunayen shugabannin riƙon ƙwaryar a shafinta na intanet.
Sai dai wani tsagin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya nemi shiga shari’ar tare da ƙalubalantar ikon kotun, inda ya ce shi ne shugabancin PDP halastacce, kuma masu ƙarar ba su da hurumin shigar da ita a madadin jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login