Connect with us

Labarai

Kotun ƙolin Najeriya ta kwace wasu manyan kadarorin Emefiele

Published

on

Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin ƙwace wasu manyan kadarori bakwai da ake alaƙanta su da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar (CBN), Godwin Emefiele.

Wannan shari’ar ta soke wani hukunci da Kotun Ɗaukaka Ƙara a Legas ta yanke a baya, inda ta bada umarnin a sake sauraron shari’ar.

Sai dai kwamitin alƙalai biyar na Kotun Koli ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Saulawa ne ya yanke hukuncin, inda ya amince da buƙatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar na soke hukuncin.

Da wannan hukunci, Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, wanda tun a ranar 1 ga Nuwamban 2024 ya ba da umarnin a ƙwace kadarorin ga gwamnatin tarayya bayan ta ce akwai gamsassun hujjojin da ke nuna cewa an mallake su ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

Emefiele dai ya ƙalubalanci umarnin ƙwace kadarorin a lokacin, amma EFCC ta ɗaukaka ƙara.

Kadarorin da kotun ta ƙwace sun haɗa da gidaje biyu da ke kan titin Hakeem Odumosu a Lekki Phase 1 a Legas, wani fili mai faɗin murabba’in mita 1,919.592 a titin Oyinkan Abayomi da ke Ikoyi, wani ƙasaitaccen gida mai lamba 65A Oyinkan Abayomi Drive, da wani gida mai ɗakuna huɗu a Probyn Road da ke Ikoyi.

Akwai kuma wani katafaren ginin masana’antu da ake ginawa a kan fili mai lamba 22 a Agbor, jihar Delta, da wasu rukunin gidaje takwas na haya a Adekunle Lawal Road da ke Ikoyi, da kuma wani gida da aka gina a kan fili mai faɗin murabba’in mita 2,217.87 a Bank Road da ke Ikoyi.

Babbar Kotun Tarayya ta kuma ba da umarnin ƙwace dala miliyan 2.45 da takardun hannun jari mallakin kamfanin Queensdorf Global Fund Limited Trust daga gareshi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!