Labarai
Babu mai kara farashin man fetur a yanzu – NNPC
Kamfanin mai na kasa NNPC ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina gaggawar sayen man fetur don tanadi sakamakon fargabar karin farashin man fetur da ake yi.
Kamfanin na NNPC ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Dakta Kennie Obateru, ya fitar a Abuja.
Wannan dai ya biyo bayan yadda ake ganin layuka a gidajen mai na kasar nan yayin da wasu gidajen man suka kasance a rufe, sakamakon fargabar da aka shiga na karin farashin man fetur din a karshen makon da ya gabata.
Obateru ya kuma gargadi dillalan man fetur da ‘yan kasuwa da su guji kara farashin man ba bisa ka’ida ba ko kuma boye shi har yayi karanci a kasuwa.
Ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su kara sa ido kan ayyukan ‘yan kasuwar da nufin hukunta wanda aka kama da irin wannan laifi na karin farashin man fetur ko boye shi.
You must be logged in to post a comment Login