Labarai
Badakalar kayan tallafi: Za mu gudanar da bincike a hukumar ‘yan gudun hijira – Muhuyi
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano za ta hada kai da ICPC don gudunar da bincike a hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa.
Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya karbi bakuncin sabon Kwamishinan hukumar ICPC mai kula da shiyyar Kano Barista Ibrahim Kagara.
Barista Muhuyi Magaji ya nuna bacin ransa kan yadda wadanda aka dorawa alhakin raba kayan tallafin suke yunkurin karkatar da akalar kayan don biyan bukatarsu, inda ya ce babu gudu babu ja da baya wajen zakulo wadanda suka aikata almundahar domin hukunta su.
A na sa jawabin tun da fari, sabon babban jami’in hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC mai kula da shiyyar Kano Barista Ibrahim Kagara, ya yi alakwarin yin aiki da hukumar karbar korafi ta jihar Kano domin yakar duk wani nau’i na cin hanci da rashawa a Kano da ma kasa baki-daya.
Barista Kagara ya ce cin hanci da rashawa wani mummunan kalubale ne da kasar nan ke fuskanta, a don haka akwai bukatar kawar da shi domin ciyar da kasar gaba.
You must be logged in to post a comment Login