Jigawa
Badaru ya soke bukukuwan sallah a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta soke yin duk wasu bukukuwa na al’ada bayan saukowa daga Sallar Idi.
Kwamishinan Lafiya kuma Shugaban kwamatin dakile yaduwar cutar Covid-19 Dr, Abba Zakari Umar ne ya bayyana haka, jim kadan bayan kammala taron tattaunwa da masu ruwa da tsaki kan lamarin.
Dr. Abba yace duk wanda zaije Sallar Idi dole ne sai ya sanya takunkumin rufe baki da hanci, sannan kuma a bada tazara a tsakanin mutane.
Kazalika Dr. Abba ya kuma kara da cewa bikin babbar Sallar zai zamo ne kamar yadda aka yi na karamar Sallah, don kaucewa yaduwar cutar corona Virus tsakanin mutane.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito cewa, mahalarta taron sun hada da sarakuna gargajiya, da kuma malamai sai yan kwamatin yaki da cutar Covid-19 da sauran masu ruwa da tsaki.
You must be logged in to post a comment Login