Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Bafulatana ta yi ikirarin kisa kan dabba

Published

on

Wata Bafulatana da ta fusata sakamakon sace mata dabba, ta sha alwashin kashe duk wanda ya dauke mata tunkiyarta mai jego matukar aka kwashe kwanaki hudu ba tare da an dawo mata da tunkiyar ba.

A tattaunawar ta da Freedom Radio, ta bayyana cewa an sha yi mata satar dabbobi, amma babu satar da ta yi mata ciwo kamar wannan, inda aka dauke tunkiyar har da dan da ta haifa.

Haka kuma ta kara da cewa, barawon tunkiyar ya yi amfani da tafiyar ta unguwa ne inda aka shiga har cikin gidanta aka zarga wa tunkiyar igiya tare da yin awon gaba da ita.

Ta ce a baya an daukar mata dabbobi har sau 6, amma yanzu an dauke mata tunkiyar ne mai kama da Rakumi, a don haka a yanzu ba za ta hakura ba kamar yadda ta hakura a baya, tana mai cewa matukar aka yi kwanaki 4 ba a dawo da tunkiyar ba, to za a samu gawar wanda ya sace ta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!