Addini
Bakin al’adu na kawo hana aure-Malam Umar Mukhtar
Na’ibin limamin masallacin Juma’a na Jami’u Zam-Zam karkashin cibiyar addinin musulunci ta Jama’atul Wa’azu Wal Irshad dake unguwar Hotoro cikin birnin Kano, ya ja hankalin al’umma da su maida hankali wajen saukakawa matasa aure, a cewarsa “shakka babu bakin al’adu suna taimakawa wajen aikata munanan ta’adu na fyade da zina a tsakanin al’umma”.
Malam Umar Mukhtar ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da wakilin Freedom Radio Umar Idris Shuaibu, jim kadan da kammala Hudubar Sallar Juma’a da ya gabatar a masallacin na Zam-Zam.
Ya ce al’umma ka iya samun sauki daga wadannan fitintinu idan aka koma kan musabbabin abin da ke kawo su.
“Idan muka soke bakin al’adu dake hana matasa daga dukkan bangarorin damar samun yin aure, wannan mataki zai taimaka.
Kwamishinoni sun bada tsagin albashin su kan yaki da Corona a Jigawa
Yadda al’ummar Dawakin Kudu suka koka kan matsalar hanya
“Addinin musulunci ya saukaka sha’anin neman aure da yinsa a tsakanin al’ummar musulmi, wanda idan aka koma kan koyarwar addinin na Musulinci zai taimaka gaya wajen rage yaduwar wadannan laifuka da suka zama ruwan dare.”
Malam Umar Mukhtar ta cikin Hudubar Sallar Juma’ar, ya ma buga misali da rayuwar magabata na kwarai ciki har da annabawan Allah da suka yi a doron kasa.
“Rayuwar annabawa na nunawa al’ummar wannan zamani cewar, rayuwa a kowane hali na kasancewa cikin jarrabawa daga Allah (S.W.T), wanda ake bukatar mumini yayi hakuri tare da tsayawa kan koyarwar addinin musulunci.”
Na’ibin limamin masallacin Juma’a na Zam-Zam din ya kuma bukaci Gwamnati da mawadata da su dauki gabarar yiwa matasa aure akan lokaci, da kuma kaucewa duk wata al’ada da zata hana wasu daga cikin al’umma damar yin aure, wata kila saboda tsadar rayuwa da aka tsinci kai a ciki.
Malam Umar Mukhtar ya kuma ja hankalin shugabanni wajen kallon laifin fyade, da kuma hukuncin da ya kamaci duk wanda ya aikata mummunar ta’adar da tayi dai-dai da koyarwar addinin musulunci.
You must be logged in to post a comment Login