Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Kwamishinoni sun bada tsagin albashin su kan yaki da Corona a Jigawa

Published

on

Kwamishinon jihar jigawa 11 sun tallafawa gwamnatin jihar da kaso goma na albashin su na watan Yuni, don cigaba da yakar corona a jahar.

Kwamishinan kudi na jihar Babangida Umar Gantsa ne ya bayyana haka ga manema labari a Dutse, a madadin sauran kwamishinonin 11.

Haka kuma Babangida Gantsa yace wannan tallafi ba shi ne na farko ba, illa kari kan na baya da suka bayar ta fuskoki daban-daban.

Wakilinmu Muhammadd Aminu Umar Shuwajo ya rauaito kwaminshinan na cewa tun lokacin da annobar Covid-19 ta shiga jihar a watan Afrilu, suke tallafawa ta wajan sayan sinadarin wanke hannu, da wayar da kai ta kafafan yada labarai kan illar cutar da matakan kariya.

Ya zuwa yanzu dai jihar Jigawa itace jiha ta 13 cikin jihohin da Coronavirus ta shiga a Najeriya wadda ke da yawan mutane kusan 310 wadda mafi yawa daga ciki sun sami waraka 8 kuma suka yi shahada.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!