Labaran Wasanni
Ballon d’or wa zai zama gwarzon dan wasa a bana ?
WA ZAI LASHE GWARZON DAN WASA A BANA, LEWANDOWSKI RONALDO, MESSI, BRUNO FERNANDEZ, MANE…?
Yayin da harkokin kwallon kafa ke ci gaba da dawowa a nahiyar turai a ‘yan kwanakin nan, wani batu da masu sharhin wasanni suka mai da hankali akai shine zaben gwarzon dan wasa na wannan shekara wanda shine zai fidda gwani na gwanaye a harkar kwallon kafa a shekara ta 2020.
Kusan shekaru da dama da suka wuce ‘yan wasa biyu ne wato Leonel Messi da Cristiano Ronaldo suka mamaye harkar kyautar ta gwarzon dan wasa a duniya.
Leonel Messi wanda dan kasar Argentina ne da ke wasa a kungiyar Barcelona a kasar Spaniya ya lashe kyautar har sau shida a baya kazalika a yanzu haka shike rike da kambun na duniya.
Leonel Messi a bana: Masu sharhin harkokin kwallon kafa suna ci gaba da tantamar anya kuwa Messi zai iya kare kambunsa a bana ganin cewa bai yi wani abin azo a gani ba a bana. To koma menene lamarin Allah ne kawai masani. MESSI dai a bana ya zura kwallaye ashirin da daya ne (21), a gasar Laligar Spaniya.
CRISTIANO RONALDO: Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal da ke wasa a kungiyar Juventus ya lashe kyautar har sau biyar a baya a kungiyoyin Manchester United da Real Madrid, haka zalika ya zura kwallaye ashirin da biyu (22) a kakar wasa ta shekarar 2019 da 2020. Kuma ana ganin yana daya daga cikin ‘yan wasa da ke kan gaba da za su iya lashe kyautar a bana matukar kungiyar sa ta Juventus ta lashe gasar Laliga da kuma gasar Zakarun Turai.
ROBERT LEWANDOWSKI: Robert Lewandowsky dan kasar Poland da ke taka leda a kungiyar Bayern Munich shine dan wasa da Ludayinsa ke kan dawo a bana. Lewandowsky dai shine dan wasa da ke kan gaba a gasar Bundesligar Jamus wajen yawan zura kwallaye. Lewandowsky dai ya ciwa kungiyar jimillar kwallaye arba’in da hudu (44), guda talatin da uku (33) a gasar Bundesliga yayin da guda goma sha daya kuma (11) a gasar Zakarun turai.
Saboda haka wasu ke ganin Lewandowsky shine dan wasa da yafi cancanta ya lashe kyautar a bana.
Labarai masu alaka.
DA DUMI-DUMI: Sadio Mane ya lasher kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika
Wa kuke ganin zai zama zakaran kwallon kafa na nahiyar Afrika a bana?
BRUNO FERNANDEZ: Bruno Fernandez dan kasar Portugal da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dan wasan tsakiya ne da a yanzu tauraronsa ke haskawa sakamakon namijin kokarin da yayi na farfado da kungiyar kwallon kafa ta Manchester united daga suma da ta yi na tsawon lokaci.
Bruno Fernadez dai a kakar wasa ta shekarar da ta wuce lokacin yana bugawa tsohuwar kungiyar sa ta Sporting Lisbon da ke kasar Portugal ya zura kwallaye talatin da biyu (32), wanda wasu ke ganin ba karamin namijin kokari yayi ba musamman ganin cewa shi dan wasa ne na tsakiya. A bana Bruno Fernandez a kungiyar Manchester United a wasanni biyar ya zuwa kwallaye uku tare da taimakawa a zura guda uku.
SADIO MANE: Sadio Mane dan kasar Senegal da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke Ingila; dan wasa ne da tun sauyin shekarsa daga kungiyar Southampton zuwa Liverpool tauraruwarsa ke ta haskawa sakamakon taimakawa kungiyar wajen lashe kofin Zakarun turai.
A bana Sadio Mane ya zuwa kungiyar Liverpool kwallaye goma sha hudu (14), a gasar Firimiyar Ingila.
CIRO IMMOBILE: Ciro Immobile dan kasar Italiya da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Lazio dan wasa ne da shima tauraruwar sa ke taka leda a bana. Duk da cewa bai shahara sosai a duniya ba, amma namijin kokarin da ya taka wajen zuwa kwallaye ashirin da bakwai a bana ya sanya muka sa shi cikin wadanda za su iya lashe kyautar a bana.
ERLING HAALAND: Erling Haaland dan kasar Norway da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund a kasar Jamus, matashin dan wasa ne da tauraruwarsa ke haskawa sakakamon yadda yake taka leda da kuma zura kwallaye ba kakkautawa.
Kafin zuwan sa kungiyar Dortmund a watan Janairun da ya gabata Erling Haaland ya zuwa kwallaye ashirin da tara ga kungiyar sa ta Red Bull Salzburg da ke kasar Austria. Tun bayan zuwan sa kungiyar Dortmund tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa sakamakon yadda yake ta zura kwallaye a raga.
Wadannan sune kadan daga cikin ‘yan wasa da nake ganin za su iya lashe kyautar gwarzon dan wasa a shekarar dubu biyu da ashirin. Idan kuna da wasu ‘yan wasan da kuke ganin sun cancanci shiga cikin wadanda na lisaffa za ku iya ba da gudunmawarku, muna maraba da hakan.
Rubutawa Abdullahi Isah.
You must be logged in to post a comment Login