Labarai
Bamu bude shafin sayar da Form ba – NDA
Kwalejin horas da kananan hafsoshin soji da ke Kaduna wato NDA ta musanta cewa ta bude shafi da ta ke sayar da form na shiga makarantar na zangon karatu na gaba.
A cewar kwalejin shafin da ke tallata fara sayar da form na shiga kwalejin na bogi ne.
Mai magana da yawun kwalejin Abubakar Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai, a Kaduna.
Sanarwar ta bukaci al’ummar kasar nan da su yi watsi da ikirarin da ke cewa kwalejin ta fara sayar da form.
You must be logged in to post a comment Login